Mutane 52 sun mutu a rikicin Sudan

Image caption Mutane sama da 50 sun mutu a rikicin Kabilanci a Sudan

Shugabannin Kabilu a yankin Darfur, sunce rikici tsakanin kungiyoyin kabilu biyu masu gaba da juna ya yi sanadiyyar kashe akalla mutane hamsin da biyu a kwanaki biyun da suka gabata.

Artabun da aka yi, tsakanin al'ummomin Miseriya dana Salamat dake kusa da iyaka da Chadi, na zuwa ne kasa da wata guda bayan da suka sanya hannun yarjejeniyar zaman lafiya.

Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya a yankin ta ce karuwar tashin hankalin kabilanci a yankin a bana, ya janyo mutanen da akai kiyasin za su kai dubu dari uku, rasa matsugunansu.

Ana kara samun Tashin hankali ne dai, game da filayen noma da ruwan sha da 'yancin albarkatun kasa, amma ana zargin dakarun gwamnati ma, nada hannu a rikice-rikicen.

Karin bayani