Tattaunawa tsakanin Israila da Palasdinu

Palestine
Image caption Shugaba Mahamoud Abbas na Palasdinu

Amurka ta ce mashawarta na Isra'ila da Palasdinawa sun amince da gayyatar da aka yi musu zuwa birnin Washington, domin tattauna batun koma wa shawarwarin neman zaman lafiya.

Tattaunawa tsakanin bangarorin biyu dai ta wargaje tun kimanin shekaru uku da suka gabata.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce za a fara ganawar ne a yammacin ranar litinin.

An tado batun ne bayan wani fadi-tashi da Sakataren harkokin wajen Amurkar John Kerry ya yi, wanda ya ziyarci yankin gabas ta tsakiya har sau 6, a cikin watanni 5 tun lokacin da ya kama aiki.

Tun farko a ranar lahadi, Majalisar ministocin Isra'ila ta amince a saki fursunonin Palasdinawa fiye da dari.

Haka nan kuma ta amince a rubuta daftarin doka dake bukatar kuri'ar raba gardama, a kan duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da Palasdinawa, wadda ta hada da batutuwan da suka shafi sassauci game da yankin kasa.