Ghana: An kuɓuto yara daga killacewar iyayensu

Image caption John Mahama, shugaban kasar Ghana

Hukumomi a birnin Accra na kasar Ghana sun kama iyayen wasu yara uku da suka killace tsawon shekaru takwas ba tare da sun yi hulɗa da kowa ba.

Yaran dai ba su san kowa ba sai iyayensu kafin sashen yaƙi da cin zarafin yara na rundunar 'yan sandan Ghana ya kuɓutar da su a ƙarshen mako a gidansu dake unguwar Madinah dake wajen birnin Accra.

Rahotanni dai na cewa, iyayen yaran sun dau wannan mataki ne domin basa son yaran su yi hulda kowanne bil'adama.

Yaran dai ba su taɓa shiga bainar jama'a sai ranar Lahadi.

Yanzu haka dai ana ci gaba da bincike akan batun.