Iraƙ: An zargi Al Qaeda da kai hare-hare

Ma'aikatar cikin gida ta Iraƙi ta zargi ƙungiyar Al-Qaida da laifin kai hare-haren bom na motoci a tsakiya da gabashin ƙasar, waɗanda suka halaka akalla mutane hamsin da ɗaya.

An kuma jiwa mutane da dama raunuka a fashe fashen bama-baman da suka tsinkayi kasuwanni da titunan dake cike da jama'a a yankunan galibi 'yan Shia yayin da ake kokarin tafiya aiki da safe.

Motocin kwana-kwana sun yi ta ƙoƙarin kai dauki bayan kai hare haren.

Wata sanarwar da aka buga a shafin yanar sadarwa na ma'aikatar tace tsanantar hare haren ya nuna irin yadda ƙungiyoyin 'yan gwagwarmaya suka samu damar kutsawa cikin al'ummar Iraƙin.

Cikin 'yan watannin nan dai Iraƙi tana fama da hare-hare da suka hallaka jama'a da dama.

Dama dai akwai matsalar saɓani tsakanin al'ummar kasar 'yan Shi da kuma 'yan Sunni.