Israila da Palasdinawa sun yi zaman farko

Image caption Wakilan Israila da Palasdinawa a zaman farko na tattaunawar zaman lafiya

Mashawarta na Isra'ila da Palasdinawa sun yi zaman farko na tattaunawar keke-da-keke tun shekaru ukku da suka gabata.

Wakilan bangarorin biyu sun gana ne a wata liyafar cin abincin dare a birnin Washington wadda Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya dauki nauyi, ya kira ta wani lokaci na musamman.

Manyan mashawartan su 2 Tzipi Livni ta Isra'ila da Saeb Erekat na Palasdinawa sun zauna dab da juna a yayinda suka fara tattauna abinda Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta kira tsarin shawarwarin da za a yi cikin watanni masu zuwa.

Shugaba Obama ya ce akwai aiki mai wuya a gaba, sai dai ya yi kira ga bangarorin biyu a kan kada su nuna son zuciya.