Al'amura sun ci gaba da gudana a Kano

Taswirar Najeriya mai nuna Kano da Abuja
Image caption A baya ma an kai hari a wata tashar manyan motocin safa a unguwar ta Sabon Gari

Rahotanni daga jihar Kano dake arewacin Nijeria sun ce al'amurra sun ci gaba da gudana kamar yadda aka saba, duk kuwa da harin Bama-baman da aka kai cikin daren Litinin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

An dai yi hada-hada a kasuwanni, yayinda kuma tituna suka cika makil da abubuwan hawa na zurga zurgar jama'a.

Rahotanni na cewa mutane da dama na can na ci gaba da karbar magani a wasu asibitoci na birnin.

Rundunar sojin Najeriya ta ce mutane 12 ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari.

Wasu ma'aikatan asibitin da BBC ta tattauna da su na nuna cewa yawan wadanda suka mutu sun zarta wadanda hukumomi suka fada, domin akwai wanda ya ce ya kirga gawarwarki 28.

Rundunar tsaro ta JTF na zargin 'yan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ne da kai harin.

An dai dana bama-baman ne a kusa da wuraren da ake sayar da barasa, a cewar wadanda suka shaida faruwar al’amarin.

Harin dai shi ne mafi muni tun bayan wani da aka kai a jihar cikin watan Junairun bara, wanda hukumomi suka ce ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200.

Karin bayani