Praministan Tunisia ya ce batun rusa gwamnati bai taso ba.

Praminista Ali Larayedh
Image caption Praminista Ali Larayedh

Praministan Tunisia, Ali Larayedh, yayi watsi da kiraye kirayen da ake yi na a rusa gwamnatin hadin gwiwar kasar.

Ya ce kamata yayi a gudanar da sabbin zabuka a ranar 17 ga watan Disamba mai zuwa.

Yayinda yake jawabi a gidan talabijin na kasar, Mr Larayedh, ya dage a kan cewa ba wai gwamnatin na son lci gaba da kasancewa a kan mulki ba ne, bayan hayaniyar da ta biyo bayan kashe manyan 'yan siyasa biyun da ake zargin cewa 'yan gwagwarmayar Islama sun yi.

Tunda farko dai, jam'iyyar Ettakatol, wadda bata da alaka da addini, wadda kuma ke cikin gwamnatin hadin gwiwar, ta yi barazanar ficewa, idan dai har ba a sake kafa sabuwar gwamnatin da ta kunshi bangarori da dama ba.

An ci gaba da artabu a garin Sidi Bouzid na kudancin kasar, garin da aka fara yin boren da ya kifar da gwamnatin da ta gabata.

Karin bayani