Masar: Ashton ta gana da Morsi

Image caption Ganar Catherine Ashton da Muhammed Morsi a watan Yuni

Babbar jami'ar tsara manufofin hulda da kasashen waje ta Tarayyar Turai, Catherine Ashton, ta gana da hambararren shugaban Masar, Mohammed Morsi, a wani wurin da ba'a bayyana ba, inda sojoji ke tsare dashi.

Baroness Ashton ta gayawa manema labarai a Alkahira cewa Mista Morsi na cikin koshin lafiya; kuma ana barinsa yana kallon talabijin da karanta jaridu.

Ashton tace"Lafiyarsa lau. Munyi tattaunawa ta kashin gaskiya cikin raha kuma a bayyane a cikin awoyi biyun dana yi tare dashi."

Ta kara da cewar sun tattauna kan bukatar ganin kasar ta Masar ta matsa gaba.

Mataimakin shugaban wucin gadin kasar, Mohammed El Baradei, ya gayawa 'yan jaridu cewa har yanzu kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta Mista Morsin na cikin tsarin harkokin siyasar kasar.

Karin bayani