An sace man fiye da dala biliyon 10 a Najeriya

Image caption Matasa masu fasa kwaurin mai a Najeriya

Hukumar dake saido a kan kudaden da ake samu daga albarkatun kasa- NEITI ta ce Najeriya ta yi hasarar harajin mai na dala biliyon goma da miliyon dari tara a cikin shekaru uku sakamakon satar danyen mai.

A cewar hukumar, lamarin satar danyen mai na janyo tarnaki wajen bukasar tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban hukumar NEITI , Mista Ledum Mitee wanda ya bayyana irin hasarar da kasar ke tafkawa, ya ce daga shekara ta 2009 zuwa ta 2011, an sace danye mai fiye da ganga miliyon 136.

Masana harkokin tsaro sun yi zargin cewar tayin la'akari da girman satar danyen mai a Najeriya inda aka kiyasata cewar ana sace akalla ganga 250 a kowacce rana, to da kamar wuya a gudanar da wannan barnar ba tare da hannu hukumomi.

Karin bayani