Isra'ila da Palasdinawa sun amince su koma tattaunawar sulhu

Erekat da Livni da Mr Kerry
Image caption Erekat da Livni da Mr Kerry

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce wakilan Isra'ila da na Palasdinawa dake taro a Washington sun amince su dukufa wajen samun dawwamammen zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya cikin watanni tara masu zuwa.

Mr Kerry ya ce za a yi tattaunawa ta ka'in da na'in cikin makonni biyu masu zuwa ko a Isra'ila ko a yankin Palasdinawa, kuma dukkan za a gabatar da dukkan muhimman batutuwan da ake neman daddalewa a kansu.

Sanarwar Amurkar ta biyo bayan shawarwarin gaba da gaba na farko da aka yi ne cikin shekaru uku tsakanin Isra'ilar da Palasdainawa.

Karin bayani