Zaɓen Zimbabwe: Ana kidayar kuri'u

Ana kidayar kuri'u na zaben shugaban kasar Zimbabwe da aka yi wanda zai yanke shawarar ko Shugaban kasar da ya fi dadewa kan mulki a Afrika Robert Mugabe zai zarce da mulkinsa na shekaru 33.

Abokin hamayyarsa Morgan Tsvangirai yana yunkuri karo na ukk ya ture shi.

Wasu rumfunan zaben dai sun kasance a bude har cikin dare don baiwa wadanda suka rage cikin layi damar kada kuri'unsu.

Bayanai sun ce mutane da dama sun fito don kada kuri'unsu.

'Yan sanda sun yi kashedin cewa duk wanda ya kwarmata ma wani sakamakon zaben zai iya shiga hannun hukuma, a yayinda ake fargabar sake fuskantar rikicin da aka yi wanda ya wargaza zaben da aka gudanar a shekara ta 2008.