Libya: An yankewa tsohon minista hukuncin kisa

Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa a kan wani tsohon minista, kuma tsohon na hannun daman hambararren shugaban kasar, Marigayi Muammar Gaddafi.

An yankewa tsohon ministan wannan hukunci ne bisa rawar da ya taka wajen murkushe masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, shekaru biyu da suka wuce.

Wakiliyar BBC a birnin Tripoli ta ce kotun ta sami Ahmad Ibrahim ne da laifin yi zagon kasa ga tsaron kasa da kuma hada baki domin hallaka fararen hula a lokacin zanga-zangar.

Wannan dai shi ne karon farko da aka samu labarin yanke wa wani kusa a tsohuwar gwamnatin kasar hukuncin kisa.

Yanzu dai wajibi ne sai kotun kolin kasar ta tabbatar da hukuncin kafin a iya aiwatad da shi.