An umurci 'yan sanda su kawo karshen zaman dirshan a Masar

Masu zaman dirshan a Masar
Image caption Masu zaman dirshan a Masar

Gwamnatin rikon kwarya ta Masar ta baiwa ma'aikatar cikin gida ta kasar umurnin ta dauki dukkan matakan da zata iya wajen kawo karshen zaman dirshan din da magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi suke yi a kusa da wani masallaci, da kuma wani dandali dake kusa da jami'ar Alkahira.

Wannan umarni dai kusan ya share fagen daukar matakin kawar da magoya bayan Muhammad Morsin dake cewa, ba zasu bar inda suke ba har sai an maida shi kan mulki.

A martaninta, Amurka ta yi kira da hukumomin Masar da su mutunta 'yancin taruwar jama'a, ciki har da zaman dirshan, tana mai cewa akwai hakki kan gwamnarin rikon kwaryar na mayar da kasar kan tsarin dimokradiyya.

Wani kakakin jam'iyyar 'Yan Uwa Musulmi ya ce zasu ci gaba da zanga zangarsu.