Boko Haram: An karawa kwamitin sulhu wa'adi

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Shugaba Goodluck Jonathan ya kara wa kwamitin da ke kokarin sulhu da 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad, wato Boko Haram, karin wa'adi na tsawon watanni biyu.

Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da wasu 'yan kasar ke sukar kwamitin a kan cewa ya gaza wajen sauke wajibcin da aka dora masa, saboda sun yi zargin cewa kwamitin ya yi ikirarin cimma yarjejeniyar dakatar da hare-hare da 'yan kungiyar, amma daga bisani shugaban kungiyar, Abubakar Shekau ya musanta.

Kwamitin ana sa bangaren ya bayyana cewa ya cimma nasarori da dama ta bangaren tattaunawa da 'yan kungiyar da kuma batun tsugunar da wadanda suka amince da shirin ahuwa.

Shugaban kwamitin, kuma Ministan ayyuka na musamman, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki ya ce mutane basu fahimci cewa aikin da suke yi abu ne da ya shafi tsaro ba don haka suna bukatar karin lokaci.

Karin bayani