'An yi watsi da bukatar hukumomin Masar'

Image caption Magoya bayan Morsi

Magoya bayan hambararren shugaban Masar Muhammad Morsi sun yi watsi da kiran da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta yi musu na su kawo karshen zaman dirshan da suke yi a wasu cibiyoyi biyu na birnin Alkahira.

Wani mai magana da yawunsu Alaa Mostafa ya ce za su ci gaba da zanga-zangar da suke yi.

Hukumomin sun ce za su ba su dama su fice daga dandali ba tare da tsangwama ba.

A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar cikin gidan ta roki masu zanga-zangar da su fifita kasar a kan duk wasu bukatu nasu.

Ta kuma yi alkawarin ba za ta hukunta su a kotu ba matukar sun bada hadin kai.

A jiya laraba ne gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan soji ta fitar da wata doka da ke bawa 'yan sanda su tarwatsa masu zanga-zangar da ke zaman dirshan.

A watan da ya gaba ta ne sojoji suka hambarar da gwamnatin demokradiya da aka zaba ta farko a kasar ta Masar, karkashin jagoranci shugaba Muhammad Morsi.

Karin bayani