An yiwa Ariel Castro daurin rai da rai

Ariel Castro
Image caption Castro ya shaidawa kotu cewa shi jarababbene

Wata kotu a Amurka, ta yanke hukuncin daurin rai da rai, da kuma karin wasu shekaru dubu a kan Ariel Castro.

Shi ne mutumin nan da ya amsa laifin cewa ya tsare wasu maata ukku a wani gida da ke birnin Cleaveland har kusan shekaru goma.

Kotun ta ce Castro, mutum ne mai matukar hadari da bai kamata a sako shi ba har iya rayuwarsa.

Tun da farko a zaman kotun, daya daga cikin maatan da Mista Castro ya tsare, Michelle Knight, ta ce ta shafe shekaru goma sha daya cikin azaba da kunci, sai dai tana fatan za ta warware daga mawuyacin halin da ta shiga.

A nasa bangare, Ariel Castro ya shaida wa kotun cewa shi ba dodo bane, yana fama da larura ne, domin Allah ya yi shi jarababbe ne.

A wani tsarin yi da wajewa da ya yi da kotun don ya kaucewa hukuncin kisa, Mista Castro ya amsa laifin aikata laifin garkuwa da mutane, fyade da kuma kisan kai.

Karin bayani