Magoya bayan Morsi na ci gaba da zanga-zanga

Egypt
Image caption Magoya bayan shugaba Morsi

Dubban magoya bayan hambararren Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi na ci gaba da zanga-zangar su a birnin Alkahira, duk kuwa da umurnin da gwamnatin da Sojoji ke mara wa baya ta baiwa 'yan sanda na tarwatsa su.

Jam'iyyar Muslim Brotherhood ta ce, ba su da wani zabi illa na ci gaba da zaman dirshan na tsawon wata guda da suke yi.

Wani kakakin kungiyar Essam el-Erian ya ce akwai fargaba ta kisan gilla idan 'yan sandan suka dauki mataki.

Ma'aikatar cikin gida na kasar ta ce za a dauki mataki sannu a hankali na fatattakar su.

Amurka ta yi kira ga Masar a kan ta girmama yancin mutane na gudanar gangami , ciki harda zaman dirshan