Dakarun Najeriya 100 sun iso daga Mali

  • 1 Agusta 2013
Image caption Dakarun tsaron Najeriya

Hukumomin Najeriya sun fara maido da wasu daga cikin sojoji sama ga dubu daya da kasar ta tura domin maido da zama lafiya a kasar Mali.

Kakakin ma'aikatar tsaro ta Najeriya, Birgadiya Janar Chris Olukolade ya shaidawa BBC cewar sama da sojoji dari daya ne suka fara isa kasar daga Mali a ranar Laraba.

A cewar hukumomin za a tura sojojin wuraren da ake da kalubalen tsaro a Najeriya.

Rundunar sojin ta ce dakarun Najeriya da za su dawo gida kusan dari bakwai ne da dori.

Najeriya ita kanta tana fuskantar matsalolin tsaro musamman a yankin arewa maso gabashin kasar inda 'yan kungiyar Boko Haram suka hana mutane sakat a jihohin Borno da kuma Yobe.

A watan Yuli ne shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku wato Borno da Yobe da kuma Adamawa a yinkurin gwamnatinsa na murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Karin bayani