Rasha ta bai wa Snowden mafaka

Image caption Edward Snowden

Ba-Amurken nan da ke guje ma kamu, Edward Snowden ya bar filin jiragen saman Moscow bayan da Rasha ta ba shi mafakar wucin gadi ta shekara daya.

An dai ce an bi da Mista Snowden ta wata barauniyar hanya ce cikin mota domin kauce ma kwakkwafin manema labaru.

Tsohon jami'in leken asirin na Amurka ya shafe makonni shidda yana ta gararamba a filin jiragen saman kasar ta Rasha bayan da Amurka ta soke fasfo dinsa.

Gwamnatin Amurkar na so ne ya koma gida domin fuskantar shari'a kan kwarmata wasu ayyukan sirri na gwamnati da suka shafi karanta ko sauraron sakonnin jama'a ta waya.

Karin bayani