'Ana hana mutane miliyon daya zabe a Zimbabwe'

Image caption Shugaba Mugabe da Pirayi Minista Morgan Tsvangira

Kungiyar sa'ido ta cikin gida a zaben shugaban kasar Zimbabwe ta ce, an hana akalla mutane miliyon daya kada kuri'arsu.

Kungiyar mai wakilai dubu bakwai ta ce wadanda ba su samu damar kada kuri'ar ba a birane galibinsu magoya bayan, Pirayi Minista Morgan Tsvangirai ne.

A cewarta masu zabe kadanne a kauyuka da ake ganin suna goyon bayan Shugaba Robert Mugabe ne, basu samu damar kada kuri'a ba.

Tuni magoya bayan Mista Mugabe suka soma ikirarin samun nasara a zaben da aka gudanar ranar Laraba.

Wani jigo a jam'iyyar Zanu-PF ta Mista Mugabe, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "sun birne jam'iyyar MDC ta Mista Tsvangirai".

Sai bayan kwanaki biyar sannan hukumar zabe za ta bayyana sakamakon zaben tsakanin Mugabe da babban dan adawa .

Masu sa'ido kan zaben daga lardunan sun yaba a kan yadda aka samun kwanciyar hankali a zaben.

Karin bayani