ZANU-PF ta yi ikirarin nasara a Zimbabwe

Image caption Magoya bayan jam'iyyar ZANU-PF

Yayin da ake ci gaba da kirga kuri'un zaben shugaban kasa a Zimbabwe, jam'iyyar ZANU-PF ta Shugaba Mugabe ta yi ikirarin samun nasara.

Babban abokin hamayya, Morgan Tsvangirai na jam'iyyar MDC ya bayyana zaben a matsayin wasan yara ne.

Mista Tsvangirai da ke yunkuri na uku na karbe shugabancin kasar daga Shugaba Robert Mugabe ya zargi jam'iyyar ZANU-PF ta Mugabe da magudin zabe da kuma razana jama'a, don haka yake ganin zaben ba shi da inganci, kuma haramtacce ne.

Babbar kungiyar da ke sa ido a zaben a Zimbabwe ta ce an samu manyan matsaloli a wannan zabe, inda mutane kusan miliyan guda ba su samu sukunin kada kuri'unsu ba.

Wannan ne karo na bakwai da Shugaba Mugabe mai shekaru tamanin da tara ke takarar shugabancin kasar.

Karin bayani