Mamayen da Isra'ila ta yi tsohon miki ne

  • 2 Agusta 2013
Image caption Imam Khamenei ya yiwa Hassan Rouhani mubaya'a

Shugaban kasar Iran mai jiran gado Hassan Rouhani, ya bayyana mamayen da Isra'ila ta yi wa yankunan Palasdinawa a matsayin wani tsohon miki.

Rouhani wanda za a rantsar da shi a ranar Lahadi, ya bayyana hakan ne a wajen wani taron gangami don nuna goyon baya ga Palasdinawa a wani bangare na bukukuwan ranar Qudus.

Sai da wasu kafofin yada labaran Iran sun ruwaito jawabin na Rouhani kashi biyu mabambamta, inda wasu suka ce ya bayyana Isra'ila a matsayin wani tsohon ciwo da dole ne a kawar da shi.

A wani martani cikin fushi, Pirayi Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Rouhani ya riga ya bayyana kansa tun da wuri.

Karin bayani