Mali: Keita da Cisse za su kara fafatawa

Image caption Soumaila Cisse da Ibrahim Boubakar Keita

Tsohon Pirayi Ministan Mali, Ibrahim Boubacar Keita shine kan gaba a zaben shugaban kasar amma dole ne sai an je zagaye na biyu.

Keita ya lashe fiye da kashi talatin da tara cikin dari na kuri'un da aka kada a yayinda Soumaila Cisse ya samu kashi 19.44 cikin dari.

Saboda Keita bai samu gagarumin rinjaye ba, a don haka za ayi zagaye na biyu na zaben tsakaninsa da Cisse a ranar 11 ga wannan watan.

Alkaluman da Ministan Mali, Moussa Sinko Coulibaly ya fitar, na nuna cewar babu dan takarar daya samu kashi hamsin cikin dari na kuri'un da aka kada.

Karin bayani