Masar: Magoya bayan Morsi sun bijire

Image caption Magoya bayan Morsi

Magoya bayan hambararren Shugaban Masar, Mohammed Morsi, na gunadar da zanga-zanga a birnin Alkahira, kwanaki biyu bayan gwamnatin dake da goyon bayan soji, ta bada umurnin a tawarwatsa masu zaman dirshan.

Ana zanga-zangar kwana guda bayanda, Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce dakarun soji na kokarin tabbatar da mulkin demokradiyya ne.

A cewarsa, abinda yasa kenan sojojin suka cire zababben shugaban Masar na farko.

Kafafen yada labaran Masar, sun ce wakilan Amurka a Gabas ta Tsakiya, William Burns zai isa birnin Alkahira nan gaba a yau Juma'a, don shawo kan matsalar siyasar kasar.

Karin bayani