Moto X : Waya mai sauraron murya

Image caption Wayoyin Moto X

Google wanda ya mallaki kamfanin wayar Motorola ya sanarda cewar zai kaddamar da wata wayar salula mai sauraron muryar me ita.

Wayar mai suna Moto X da zarar an ce "OK Google now...." za ta jira umurnin da me wayar zai bata.

Wayar wacce za a kera a Amurka, za a baiwa kwastomomi damar sarrafata yadda suke so.

Wayar ce za ta kasance ta farko da kamfanin zai kera, tun bayan da Google ya siya Motorola a kan dala miliyon goma sha biyu da rabi a shekarar data wuce.

Goggaya a Kasuwa

Masu sharko sun ce fito da wayar, zai kasance matsala ga kasuwar wayoyi masu amfani da manhajar Android, saboda sauran kamfanonin dake mu'amala da Google za su iya cin karo da matsalar karancin riba.

Za a dinga kera wayar Moto X ne a birnin Texas na Amurka.

Wayar Moto X ce waya ta farko da Google zai kera tun da ya mallaki kamfanin a watan Mayun bara.

Kamfanin ya fitar da wasu wayoyi a baya, amma wadanda wasu kamfanonin suka taimaka wajen kera masa ne.

Wannan na nufin cewar Google nason taka rawa a kasuwar wayoyin salula.

Karin bayani