Kaka ta sayar da jikarta

Image caption Wata jaririya

Jami'an tsaro a jihar Filato dake arewacin Najeriya sun tsare wasu mata biyar bisa zarginsu da sayarda jaririya 'yar watanni shida.

A cewar hukumomin sun ceto jaririyar ce a jihar Anambra dake kudancin Najeriya bayan da kakarta jaririyar ta sayar da ita a Jos .

Jami'an tsaron sun ce an sayar da jaririyar a mataki daba-daban wato dillalai daban-daban suka shiga cinikin.

'Yan sanda sun ce kakar jaririyar ta sayar da jaririyar ce ga wata mai suna Eucharia Anyeagbu, a kan kudi naira dubu dari biyu.

Kwamishinan 'yan-sandan jihar ta Filato, Mista Chris Olakpe, ya ce an yi cinikin ne hawan-hawa, daga karshe dai an sayar da jaririyar kan kudi naira dubu dari biyar da talatin ne ga wata mai suna Grace Nnadozie.