Amurka za ta rufe wasu ofisoshin jakadancinta

Image caption Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry

Amurka za ta rufe wasu daga cikin ofisoshin huddar jakadancinta dake kasashen duniya a ranar Lahadi, saboda batun da ya shafi tsaro.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce, rufe ofisoshin na ta da akasari wadanda ke kasashen musulmi ne.

Ta kuma ce mataki ne na kandagarki game da barazanar da muradunta ke fuskanta a kasashen waje.

Mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar, Marie Harf ta ce, ma'aikatar ta bayar da umarnin cewa wasu daga cikin ofisoshin huddar jakadancin manya da kanana, za su kasance a rufe ranar Lahadi 4 ga watan Ogusta.

Ta ce an dauki wannan mataki ne don kare ma'aikatanta, dama masu ziyartar ofisoshin nata daga fuskantar duk wata barazana.

Kana mai yiwuwa ne a kara yawan kwanakin rufe wadannan ofisoshi, wanda ya danganta ga yadda aka samu bayanai daga ofisoshin daban-daban, kan ko sun iya aiwatar da wadannan matakai.

Dama dai Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta sha fuskantar zarge-zarge, game rashin samar da isasshen tsaro a ofisoshin jakadancin kasar.

Wannan ya biyo bayan wani hari da aka kai kan karamin ofishinta dake birnin Benghazi na kasar Libiya, a cikin watan Satumbar bara, da yayi sanadiyyar mutuwar jakadan Amurkar, da wasu daga jami'anta.