Utaka ya koma Sivasspor a Turkiya

Image caption John Utaka na murnar nasara

Kungiyar Sivasspor ta tabbatar da sayen dan Najeriya John Utaka daga kungiyar Montpellier ta Faransa.

Dan shekaru talatin da dayan ya koma kungiyar ta kasar Turkiya a yarjejeniyar shekaru biyu da rabi bayan an tabbatar da lafiyarsa.

Utaka yace" na zo wannan kulob dinne don in samu nasara".

Utaka ya lashe gasar Faransa ta Ligue 1 tare da Montpellier a shekara ta 2012 kuma ya bugawa babbar tawagar kasa ta Najeriya wasanni sau 43.

Ya kuma lashe gasar kofin FA na Ingila tare da Portsmouth a shekara ta 2008.

Utaka ya soma taka leda ne a Enugu dake gabashin Najeriya, kafin yaje Masar inda ya bugawa kungiyoyin Arab Contractors da Ismaily, sai kuma kulob din Al-Sadd a kasar Qatar.

A kasar Faransa kuwa, ya bugawa kungiyoyi uku wato Lens da Rennes da kuma Montpellier sai kuma kungiyar Portsmouth ta Ingila.

Karin bayani