An fara fitar da sakamakon zabe a Zimbabwe

Kirga kuri'u a zaben kasar Zimbabwe
Image caption Kirga kuri'u a zaben kasar Zimbabwe

Hukumar zabe a Zimbabwe ta fara fitar da sakamakon zaben kasar, sa'oi kadan bayan shugaba Robert Mugabe na jam'iyyar Zanu-PF ya ayyana samun gagarumar nasara.

Babban abokin adawar Mr.Mugabe, Morgan Tsvangirai ya bayyana zaben a matsayin shirme.

Ya ce barazanar da aka yiwa mutanen su da kuma magudin da aka aikata sun kawar da ingancin zaben.

Babbar kungiyar da ke sanya ido a zaben na Zimbabwe ta ce an aikata ba dai-dai ba a zaben, inda mutane da yawa ba su samu damar kada kuri'ar su ba.