Jam'iyyar ZANU-PF ta lashe zaben majalisa

Image caption Jagoran jam'iyyar ZANU-PF Mr Mugabe

Hukumar zaben kasar Zimbabwe ta ce jam'iyyar ZANU-PF ta Shugaba Robert Mugabe ta lashe kusan kashi biyu cikin uku na kujeru majalisar dokokin kasar.

Wannan gagarumar nasara ta ishi jam'iyyar ta yiwa kundin tsarin mulkin kasar garan bawul.

Kawo yanzu dai ba a bayyana sakamakon zaben shugaban kasa ba tsakanin Mista Mugabe da Morgan Tsvangirai.

Jam'iyyar adawa ta MDC wacce ta fafata da ZANU-PF, ta ce ba zata amince da sakamakon ba, bisa zargin tafka magudi.

Twagogin sa'ido kan zaben na kasashen Afrika, sun amince da irin yadda akan gudanar da zabukan, duk da cewar akwai 'yan matsaloli kan batun rijistar masu kada kuri'a.

Mista Mugabe dan shekaru tamanin da tara, na kokarin darewa mulki a karo na bakwai.

Karin bayani