Kungiyar AU ta yaba da zaben Zimbabwe

Image caption Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

Shugaban tawagar sa ido ta kungiyar tarrayyar Afrika a Zimbabwe, Cif Olusegun Obasanjo ya ce zaben da aka gunadar a ranar Laraba an yi cikin gaskiya da adalci.

Obasanjo ya ce akwai wasu 'yan matsaloli da aka fuskanta lokacin kada kuri'a amma basu kai su shafi sakamakon daukacin zaben ba.

Sakamakon farko na nuna cewar Shugaba Robert Mugabe na jam'iyyar ZANU-PF na ikirarin samun galaba.

Babban abokin hammayarsa, Morgan Tsvangirai ya bayyana zaben a matsayin wasan yara.

Kungiyar data fi kowacce girma a Zimbabwe wajen sa'ido akan zaben a ranar Alhamis ta ce an yi cuwa-cuwa sosai a zaben, inda tace mutane da yawa ba su samu damar kada kuri'ar su ba.

A ranar Laraba ne aka gudanar da zaben Shugaban kasa, da kuma na 'yan majalisar dokoki da kansiloli su 210 a kasarta Zimbabwe.

Hukumar zaben Zimbabwe-ZEC nada kwanaki biyar ta bayyana wanda ya lashe zaben.

Karin bayani