Nijar ta cika shekaru 53 da samun 'yanci

Jamhuriyar Nijar
Image caption Nijar ta samu ci gaba a wasu fannoni cikin shekaru 53

A yau ne jamhuriyar Nijar ta cika shekaru 53 da samun 'yancin kai daga hannun turawan mulkin mallaka na kasar Faransa.

A cikin wadannan shekaru dai an samu cigaba a bangarori da dama musamman ta fannin dimokradiyya, wanda ya baiwa 'yan kasar damar fadin albarkacin bakin su.

Shugaban Kasar Muhammadou Issufou ya gabatar da jawabi ga 'yan kasar akan zagoyowar ranar samun 'yancin kan kasar.

A cikin jawabin nasa Shugaba Issoufu ya ce gwamnatin sa ta gudanar da wasu sauye sauye domin farfado da tattalin arzikin kasar ta fannonin da dama da suka hada da aikin gona da kiwon lafiya da ilimi da samar da ruwan sha da dai sauransu.

A baya dai Nijar ta fuskanci matsalolin da suka hada da karancin abinci da gurgusowar hamada da kuma tsaro.

Karin bayani