Sun ce a yankewa 'yan fashin teku uku hukunci

Wani dan fashin teku a kasar Somalia
Image caption Wani dan fashin teku a kasar Somalia

Wasu masu taimakawa alkali a jihar Virginia ta Amurka sun bukaci da a yankewa wasu 'yan fashin tekun Somalia hukuncin daurin rai da rai.

'Yan fashin dai sun hallaka wasu Amurkawa hudu, a jirgin ruwansu a shekarar 2011 a gabar tekun Afrika ta gabas.

Amurkawan sun hada da wasu ma'aurata Scott da Jean Adam, da abokan tafiyarsu biyu.

Wasu daga mutane goma sha daya da ake tuhuma da aikata irin wannan laifin dai tuni suka fara zaman wakafi a gidan yari.

'Yan fashin sun yi aniyar tasa keyar Amurkawan zuwa kasar Somalia ne su kuma nemi makudan kudaden fansa.

Yayinda sojin ruwan Amurka suka fara bin jirgin nasu ne, nan take suka bindige dukkannin Amurkawan hudu.

Wannan dai ita ce shari'ar 'yan fashin teku ta farko da masu gabatar da kara na Amurka suka bukaci a yanke hukuncin kisa.