Amurka ta gargadi matafiya 'yan kasarta

Jami'an tsaron filin saukar jiragen sama a Amurka
Image caption Jami'an tsaron filin saukar jiragen sama a Amurka

Amurka ta gargadi 'yan kasarta a duk fadin duniya cewa, ta yiwu kungiyar Al-qaeda su kai hari a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta ce, akwai yiwuwar a kai hari a wuraren da 'yan yawon bude ido ke taruwa ko kuma ababen hawa na jama'a a cikin watan Agustan nan.

Wannan na zuwa ne bayan da Amurkar ta fitar da sanarwar cewa za ta rufe ofisoshin huddar jakadancinta fiye da 20 dake wasu kasashen musulmi a ranar Lahadi.

'Yan majalisun dokokin Amurkar dai sun ce, wannan gargadi ba shi da wani banbanci da abubuwan da aka saba ji game da batun barazanar tsaron kan muradun kasar a wasu kasashen.

Amma kuma Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce ta dauki wannna mataki ne kan abinda ta kira yin kandagarki.

Tana mai gargadin matafiya da su yi taka tsan-tsan, musamman ma a motocin haya da kuma wuraren yawon bude ido.

Wannan gargadi ga matafiyan dai wanda zai ci gaba da kasancewa har ya zuwa karshen watan Ogusta, na zuwa ne kasa da shekara guda bayan wani hari da aka kai kan karamin ofishin huddar jakadancin Amurka a birnin Benghazi na kasar Libya.

Harin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'anta da suka hada da jakadan kasar a Libya, Christopher Stevens.