Mugabe ya lashe zaben Zimbabwe

Mugabe ya lashe zabe

Hukumar zaben Zimbabwe ta sanar da Robert Mugabe a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Mugabe ya samu kashi 61 ne bisa bisa dari na kuri'un da aka kada.

Babban abokin hamayyar sa Morgan Tsvangirai ya samu kusan kashi 34 na kuri'un.

Sai dai Mista Tsvangirai ya yi wasti da sakamakon zaben yana mai cewa zai kalubalance shi a kotu

Mista Tsvangirai ya kuma ce jam'iyyar sa ta MDC ta raba gari da jam'iyyar ZANU-PF.

Jam'iyyun biyu dai sun amince ne su yi aiki tare a wani tsarin gwamnatin hadaka bayan zaben kasar na shekarar 2008 wanda ya haddasa tashin hankali.

Karin bayani