Mutane 13 sun mutu a hadarin mota a jihar Filato

Hadarin Mota a Najeriya
Image caption Hadarin Mota a Najeriya

Hukumomin a jihar Filaton Najeriya sun ce mutane 13 ne suka rasu , yayin da tara suka jikkata a wani hadarin mota a kauyen Barkin Ladi.

Kakakin rundunar yansandan jihar ta Filato DSP Felicia Anslem, ta shaidawa BBC cewa hadarin motar ya auku ne a cikin garin Barkin Ladi, kan hanyar Bokkos.

Ya kuma rutsa da samarin kungiyar Boys Brigade, dake atisaye.

Wata mota kirar Wagon samfurin 505 ce ta kwace wa direban ta murkushe samarin.

Wani rahoto na hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai ya nuna cewa, Najeriya ita ce kasa ta biyu da aka fi samun hasarar rayuka da jikkata a sanadiyar hadduran hanya bayan kasar Indiya, inda dubban mutane kan rasa rayukansu a duk shekara.

Akasari dai ana dora laifin yawan haduran mota a Najeriya da tukin ganganci, da rashin kyawun hanyoyin mota.