Rouhani ya yi alkawarin kwatanta adalci

Image caption Rouhani ya yi alkawarin kawar da cin hanci da rashawa

Sabon shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su kawo karshen takunkumin da suka sanyawa kasarsa.

Mr Rouhani ya kuma yi alkawarin samar da karin dama ga mata da kuma dakile cin hanci da rashawa

Sabon shugaban ya ce al'ummar Iran na bukatar ci gaba da kuma canji.

Ya ce suna kuma son a girmama su, a kuma ba su kima tare da bukatar rayuwa a yanayi na 'yanci.

An gudanar da bikin rantsuwar a majalisar dokokin kasar, wanda ya samu halartar wasu shugabannin kasashen duniya da kuma wakilan kasashe da dama.

Karin bayani