An rantsar da Hassan Rouhani

Hassan Rouhani
Image caption Hassan Rouhani ya yi alkawarin maido da martabar Iran

An rantsar da Hassan Rouhani a matsayin sabon Shugaban Kasar Iran.

Mr. Rouhani ya dau alkawarin inganta tattalin arzikin Kasar da samarwa da dukkanin Iraniyawa adalci da kuma 'yanci kamar yadda tsarin mulkin Kasar ya tanadar.

Sabon Shugaban ya kuma lashi takobin kare iyakokin kasar.

Mr Rouhani ya kuma yi alkawarin samar da karin damammaki ga mata da kuma dakile cin hanci da rashawa

Sabon Shugaban ya kuma ce al'ummar Iran na bukatar ci gaba da kuma canji. Ya ce suna kuma son a girmama su, a kuma basu kima tare kuma da bukatar rayuwa a yanayi na 'yanci.

An gudanar da bikin rantsuwar a majalisar dokokin Kasar, wanda ya samu halartar wasu Shugabannin Kasashen duniya da kuma wakilan Kasashe da dama.

Karin bayani