Saudiyya ta hana Al-Bashir shiga sararin samaniyar ta

Omar Al-Bashir
Image caption Dangantakar Saudi Arabia da Sudan ba mai kyau bace

Hukumomi a Sudan sunce an hana Shugaban Kasar Sudan Omar al Bashir shiga ta sararin samaniyar Saudi Arabiya, abinda yasa ala tilas ya koma Khartoum.

Mr al-Bashir dai yana kan hanyarsa ne ta zuwa Iran domin ya halarci bikin rantsuwar sabon Shugaban Kasar Hassan Rouhani.

Kasar Saudi Arabiya, wacce bata dasawa da Iran, bata bada dalilin daukar wannan mataki ba.

Kotun manyan laifuka ta duniya dai na neman Mr. Al-Bashir ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan yaki da kuma kisan kare dangi.

A watan da ya gabata Najeriya ta yiwa Al-Bashir kyakyawar tarba a lokacin da ya halarci taron kungiyar Tarayyar Afirka

Karin bayani