Za a rantsar da Robert Mugabe

shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Image caption Za a rantsar da Robert Mugabe a karo na bakwai

A yau za a rantsar da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a karo na bakwai a matsayin shugaban kasa.

An ayyana ranar ta yau ta zama hutu dan bawa magoya bayan Mr Mugabe dan shekaru tamanin da tara damar halartar bikin rantsarwar da za a yi a filin wasa da ke Harare.

An dai samu tsaikon rantsar da shi ne sakamakon karar da abokin hamayyarsa Morgan Changarai ya shigar.

Kan cewa an yi magudi a lokacin zaben, amma sai kotun tsarin mulki ta kori karar.

Mr Mugabe dai shi ne prime minista na farko a kasar bayan bada mulki tsakanin alif dari tara da tamanin zuwa alif dari tara da tamanin da bakwai, kuma tun daga lokacin ya zama shugaban kasar kawo yanzu.

Karin bayani