Boko Haram: Mutane 35 sun mutu a Borno

Image caption Abubakar Shekau na Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce mutane akalla talatin da biyar sun mutu sakamakon bata kashi a wajaje biyu da 'yan Boko Haram a ranar Lahadi.

Rundunar sojin ta ce lamarin farko ya faru ne a barikin 'yan sanda dake garin Bama dake gabda kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Lamari na biyu ya faru ne a garin Malam Fatori duk a cikin jihar ta Borno.

Jihar Borno ta kasance fagen daga tsakanin jami'an tsaron Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram masu tada kayar baya.

A watan Mayu ne Shugaba Jonathan ya ayyana dokar ta baci a jihohi uku dake arewa maso gabashin Najeriya a yinkurin murkushe 'yan Boko Haram.

Karin bayani