Fonterra ya nemi afuwa a China

Alamar Kamfanin Fonterra
Image caption Alamar Kamfanin Fonterra

Kamfanin madara na kasar New Zealand Fonterra ya nemi afuwar masu sayen kayansa a China bayan farbagar cewa kayansa na kunshe da wani abu da zai iya sa cuta, ya sa an janye kayan daga kasuwa.

Shugaban kamfanin, Theo Spierings, ya garzaya zuwa Beijing ya nuna nadama saboda yadda lamarin ya haddasa damuwa.

Ranar Asabar ne dai kamfanin ya bayyana cewa, mai yiwa kwayoyin cuta sun gurbata madarar da yake yi, kuma za ta iya haddasa cuta a jikin jarirai.

Tuni dai jama'a suka soma tofa albarkacin bakinsu akan lamarin inda wasu ke nuna damuwa matuka, suna masu cewa yanzu dole su kara yin taka tsantsan wajen zabar irin madarar da za su saye.