Kokarin warware takaddamar siyasa a Masar

Image caption Jami'an Diplomasiyya a Masar

Ana ci gaba da kokarin diplomasiyya don kawo karshen rikicin siyasar Masar, inda a yau 'yan majalisar dattijjan Amurka, John McCain da Lindsey Graham za su je birnin Alkahira.

A karshen mako, mataimakin Sakataren harkokin wajen Amurka, William Burns ya tsawaita ziyararsa a kasar, inda ya gana da babban hafsan sojin Masar, Janar Abdel Fattah al-Sisi da Pirayi Minista Hazem Beblawi da kuma wakilan kungiyar Muslim Brotherhood.

Ana ci gaba da zaman dar dar, bayan da hukumomi suka bukaci magoya bayan Muhammed Morsi wadanda ke son a maidodashi kan mulki, su kawo karshen zanga-zangar da suke yi.

Ministan harkokin wajen Qatar dana haddadiyar daular Larabawa suma suna cikin tattaunawar kuma rahotanni sun nuna cewar sun gana da mataimakin shugaban Muslim Brotherhood, Khairat el-Shater.

Karin bayani