Gervinho da Chamakh sun bar Arsenal

Image caption Gervinho da Marouane Chamakh

'Yan wasan Arsenal Gervinho da Marouane Chamakh sun bar kulob din kamar yadda kocin kungiyar Arsene Wenger ya bayyana.

Dan kasar Ivory Coast Gervinho, wanda ya hade da Gunners a kan pan miliyon 11 daga Lille a shekara ta 2011, ya koma AS Roma ne a kan pan miliyon 6 da dubu dari tara.

Chamakh, wanda ya zo Arsenal daga Bordeaux a shekara ta 2010, zai koma Crystal Palace ne.

Wenger yace "Gervinho ya koma Roma a yayinda Chamakh ke hanyarsa ta zuwa Crystal Palace".

Gervinho mai shekaru 26 ya zira kwallaye 11 a wasanni 63 daya bugawa Arsenal.