Matsala a tashar nukiliya ta Fukushima

Image caption Ana kokarin shawo kan matsalar

Hukumar kula da makamashin nukiliyar Japan ta ce tashar samar da makamashin nukiliya ta Fukushima, na fuskantar wani yanayin gaggawa saboda irin tiririn dake tasowa daga ruwan dake karkashinsa.

Hukumar ta yi gargadin cewar idan har ba a magance matsalar ba a cikin makwanni uku, tabbas gurbataccen ruwan zai iya kwarara zuwa tekun Pacific.

Injiniyoyi suna ta kokarin gina wani rami ta kasa don gurbataccen ruwan ya shiga.

kawo yanzu ruwan na kara tafasa kuma yana karuwa sosai.

Gwamnatin Japan ta bukaci masu lura da tashar wato TEPCO su dauki mataki.

Karin bayani