Magoya bayan Mugabe sun farmana- MDC

Image caption Shugaba Mugabe da Morgan Tsvangirai

'Ya'yan jam'iyyar adawa a Zimbabwe-MDC sun ce magoya bayan Shugaba Robert Mugabe sun kai musu hari.

Zargin na zuwa ne kwana guda, bayan da aka sanarda sakamakon zaben shugaban kasar a hukumance, inda Mista Mugabe zai cigaba da mulki a wa'adi na bakwai sannan jam'iyyarsa ZANU-PF ta samu gagarumin rinjaye a majalisar dokokin kasar.

'Yayan jam'iyyar MDC su 11 a Harare da kuma wasu 20 a lardin tsakiyar Mashonaland sun ce tunda aka sanarda sakamakon, 'yan Zanu-PF ke kai musu hare-hare.

Kakakin Zanu PF Psychology Maziwisa ya karyata zargin harin.

Shugaban MDC, Pirayi Minista Morgan Tsvangirai ya sha alwashi kalubalantar sakamakon zaben a kotu.

Karin bayani