Sarkin Musulmi ya yi bude-baki da Kiristoci

Image caption Sarkin Musulmi, Muhammed Sa'ad

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya yi bude-bakin azumin watan Ramadana tare da shugabannin Kirista a fadarsa dake Sokoto.

Ana kallon matakin a matsayin wani yinkurin kara maido da fahimta da yarda da juna tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya, dake yawan fuskantar tashin hankali a 'yan shekarunnan.

Sarki Sa'ad wanda shine Shugaban Majalisar koli ta addinin Islama a Najeriya ya gayyaci shugabannin Kiristocinne na kungiyar hadaka ta Peace and Reconciliation Foundation.

Shugabanin Kiristocin sun yaba da matakin, inda suka ce hakan zai kara wanzar da zaman lafiya a kasar.

Najeriya na fuskantar tsaka mi wuya saboda rashin jituwa tsakanin mabiya addinnan kasar.

Karin bayani