Ana kai ruwa rana tsakanin Atiku da PDP

Alhaji Atiku Abubakar
Image caption Alhaji Atiku Abubakar

A Najeriya, tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar ya koka cewa jam'iyyarsa ta PDP mai mulkin kasar na neman yi masa kora-da-hali.

Ya yi zargin cewa jam'iyyar ba ta ba shi matsayi da sauran alfarmomin da kundin tsarin mulkin ta ya kebe ma sa ba.

Hakazalika Alhaji Atiku Abubakar ya yi korafin cewa jam'iyyar ba ta sanya sunansa a cikin wadanda za su wakilce ta a babban taron da ta shirya yi a karshen wannan watan ba.

Sai dai jam'iyyar a nata bangaren ta musanta wannan zargi, tana cewa ba a fitar da jerin sunayen mahalarta taron ba tukunna, ballanta wani ya ce an cire shi.

Karin bayani