Bincike kan cinikin makamai a Afirka ta Kudu

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma
Image caption Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma

Hukumar bincike kan cinikin makamai a Afirka ta kudu da aka dade ana jira, yanzu haka ta fara gudanar ta aikinta a birnin Pretoria.

Hukumar wacce shugaba Jacob Zuma ya kafa ta a watan Oktobar shekara ta 2011, an kudiri fara gudanar da aikinta a cikin watan Maris.

Amma kuma sai aka jinkirta don bai wa masu gudanar da binciken isasshen lokacin da zasu kammala aikinsu.

An dai dorawa wannan hukuma alhakin gudanar da binciken zargi kan cin hanci da rashawa da ya shafi badakalar cinikin makamai a kasar.

Amma kuma sai aka jinkirta don bai wa masu gudanar da binciken isasshen lokacin da zasu kammala aikinsu.

Shi kan shi shugaba Jacob Zuma an tuhume shi da aikata laifin cin hanci da rashawa da ke da alaka da cinikin makaman.

Wannan ya biyo bayan daure tsohon mai bashi shawara kan harkokin kudi Schabir Shaik, wanda aka samu da laifin shigewa Mr Zuma gaba, wajen karbar cin hanci daga Kamfanin kera makamai na kasar Faransa,

Kashin farko na aikin hukumar binciken dai zai kai har ya zuwa karshen watan Nuwamnba ne, amma kuma shugaban Jacob Zuma na kokarin amincewa da bukatar karin wa'adin shekara guda.