Kotu ta sami Janar a Turkiya da laifi

Image caption Kotu ta ce Janar Basbug ya ci ammanar kasa

An yankewa tsohon babban hafsan sojin kasar Turkiya hukuncin daurin rai-da-rai a gidan kaso, bisa zargin kokarin kifar da gwamnati.

Janar Ilker Basbug shine mutumin da yafi fice daga cikin mutane dari biyu da saba'in da biyar da ke fuskantar shari'a bisa zargin hannu a kokarin hambarar da gwamnatin kasar mai kishin Islama.

Sai dai a shari'ar da aka shafe kusan shekaru biyar ana yi, kotun ta wanke wasu daga cikin wadanda ake zargin, a yayinda wasu kuma aka yanke musu hukuncin dauri a gidan yari.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar nuna rashin amincewa da shari'ar a birnin Santabul.

Karin bayani